Halakar Sojojin Hayar Saudiyya 10 A Lardin Ta'az Na Kasar Yamen

Halakar Sojojin Hayar Saudiyya 10 A Lardin Ta'az Na Kasar Yamen

Sojojin Yamen da dakarun Ansarullahi sun kashe sojojin hayar masarautar Saudiyya akalla 10 a lardin Ta'az da ke kudu maso yammacin kasar ta Yamen.

Majiyar rundunar sojin Yamen ta sanar da cewa: Sojojin Yamen da hadin gwiwar dakarun sa-kai na kasar sun kai wani harin kwanton bauna kan tawagar sojojin hayar masarautar Saudiyya a yankin Asifarah da ke lardin Ta'az a jiya Asabar, inda suka yi nasarar halaka sojojin akalla 10 tare da jikkata wasu adadi mai yawa.

A gefe guda kuma jiragen saman yakin masarautar Saudiyya sun yi luguden wuta kan yankin Annajibah da ke gabashin garin Al-Makha a lardin na Ta'az, inda suka rusa gidajen fararen hula amma babu cikakken labarin irin hasarar rayukan da hare-haren suka janyo.   


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky