Girgizar kasa ta hallaka sama da mutane 370 a Indonesia

Girgizar kasa ta hallaka sama da mutane 370 a Indonesia

Akalla mutane 384 sun rasa rayukansu, wasu 540 suka jikkata, sai kuma mutane 29 da suka bata, sakamakon girgizar kasar da ta afkawa garin Palu da ke tsibirin Sulawesi na kasar Indonesia a jiya Juma’a.

Girgizar kasar mai karfin maki 7.5 a ma’auninta na Ritcher, ta haddasa ambaliyar ruwa da ta kutsa cikin garin, kuma rahotanni sun ce, har ya zuwa safiyar yau, kasa ta cigaba da motsawa, lamarin da ya haddasa dagawar igiyar ruwa da tsawon mitoci biyu da ya sake antayawa garin na Palu.

A jiya Juma’a ma dai girgizar kasar ta jawo dagawar igiyar teku zuwa tsawon mitoci akalla 6, wadda ta haddasa mummunar ambaliyar ruwa, a garin na Palu.

Kakakin hukumar bada agajin gaggawa na Indonesia, Sutopo Nugroho, ya ce mafi akasarin mutanen da aka gano gawarwakinsu a warwartse, sun hallaka ne, sakamakon gine-ginen da suka fada musu.

A watan Agustan da ya gabata girgizar kasa ta hallaka mutane 500 a tsibirin Lombok na kasar ta Indonesia, inda ta rusa daruruwan gidaje.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky