Fursunonin Palastinawa Sun Dakatar Da Yajin Cin Abinci

Fursunonin Palastinawa Sun Dakatar Da Yajin Cin Abinci

Palastinawan da ke yajin cin abinci a gidajen kason Isra'ila sun kawo karshen yajin cin abincin nasu a yau bayan cimma yarjejeniya kan hakan.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, bayan kwashe tsawon kwanaki 40 fursunonin Palastinawa kimanin 1800 suna yajin cin abinci a yau da aka shiga kwana na 41 sun kawo karshen yajin cin abincin, bayan da haramtacciyar kasar Isra'ila ta amince ta saurari korafe-korafensu.

Palastinawan sun kokawa ne kan halin matsi da suke cikia  wuraren da Israila ake tsare da su, da dama daga cikin fursunonin dai Isra'ila na tsare da su ne bisa akidarsu ta gwagwarmaya da kin amincewa da zalunci da kuma mamayar da take yi musu, da suka hada har da mata da kuma kanan yara.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky