An zargi Faransa da goyon bayan ta'addancin Syria

An zargi Faransa da goyon bayan ta'addancin Syria

Ministan harkokin wajen Faransa ya yi watsi da kalaman shugaban Syria Bashar Assad da ke zargin Faransa da taimakawa ayyukan ta’addanci, tare da cewa ba za ta iya taka rawa domin warware rikicin kasarsa ba.

Yayin zantarwarsa da manema labarai a birnin Damascus, Assad ya kuma bayyana Kurdawan kasar da ke samun goyon bayan kasashe irinsu Amurka a matsayin munafukai.

Assad ya ce Munafunci matsayi ne da ya hau kan wuyan dukkanin wani wani dan kasar Syria dake yi wa wata kasa ta ketare aiki, musaman rundunar sojan Amruka.

An kiyasta cewa, Kurdawa da ke da yawan kimanin kashi 15 cikin dari na alúmmar Syria, sun hau matsayin yan ba ruwammu ne a fadan da ake gwabzawa tsakanin gwamnatin da yan tawaye. Daga bisani ne suka amfana da tabarbarewar lamura a Syrian, suka kuma samu damar shata kwarya kwaryar yancin cin gashin kan yankin nasu dake arewa maso gabashin kasar.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky