Gwamnatin Obama ta yi mani sata- Trump

Gwamnatin Obama ta yi mani sata- Trump

Shugaban Amurka, Mista Donald Trump, ya zargi gwamnatin Obama da ta shude da satar bayanan wayarsa a babban ginin nan nasa da ake kira Hasumiyar Trump dake birnin New York, gab da lokacin samun nasararsa a zaben shugaban kasar da aka yi a shekarar da ta gabata

A wani jerin sakwannin Tweeter, Mista Trump, bai bayar da wata shaida ko hujja ba game da zargin, amma ya bayyana satar bayanan wayar tasa a matsayin mummunan al'amari.

Ya kuma bayyana Barack Obama a matsayin ''mutumin banza''.

Rahotannin kafofin watsa labarai na baya-bayan nan sun nuna cewa hukumar bincike ta FBI ta nemi takardar izini domin sa ido a kan mukarraban Trump wadanda ake zargi da yin huldar da ba a saba yin irinta ba da kasar Rasha.

Kawo yanzu dai fadar gwamnatin Amurka bata ce uffan ba, kana fishin Mista Obama bai mayar da martani ba.

To amma wani 'dan majalisar wakilan Amurka na jam'iyyar Dimokurat ya ce shugaban kasa baya bayar da izinin satar bayanan sadarwar waya, alkalai ne kan yi.

A lokacin yakin neman zaben shugaban kasa, an samu rahotanni a watan Mayun bara cewa ma'aikatan Mista Trump sun ce suna jin ana satar tatsar bayanai a ofisoshinsu dake ginin na Hasumiyar Trump a birnin New York.

A watan Janairu ne Mista Barack Obama dan jam'iyyar Dimokurat, ya mika wa Mista Donald Trump, dan jam'iyyar Republican shugabancin Amurka.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky