An Yi Maraba Da Murabus Din Nikki Haley

An Yi Maraba Da Murabus Din Nikki Haley

Rahotanni sun bayyana cewar cibiyoyin kasa da kasa musamman na kare hakkokin bil'adama sun yi maraba da kuma nuna jin dadinsu dangane da murabus din da tsohuwar jakadiyar Amurka A MDD, Nikki Haley, ta yi a jiya

Cikin wata sanarwa da ta fitar, Kungiyar kare hakkokin bil'adama ta Amnesty International ta bayyana cewar murabus din da Nikki Haley din ta yi wani abin maraba da shi ne don kuwa a lokacin da take rike da wannan mukamin kungiyoyin kare hakkokin bil'adama da dama sun fuskanci matsin lamba da kuma nuna wariya daga wajenta.

Shi ma a nasa bangaren jakadan kasar Bolivia a MDDn Sacha Yorenti yayin da yake magana kan murabus din tsohuwar jakadiyar Amurkan ya bayyana cewar kasarsa tana adawa da irin yadda Amurka, ta hanyar jakadiyar nata take karen tsaye ga dokoki da yarjejeniyoyin na kasa da kasa ciki kuwa har da yarjejeniyar nukikiya na Iran da kuma na batun dumamar yanayi.

Shi ma jakadan kasar Sweden a MDD, Olaf Skog ya bayyana fatan sabon jakadan Amurka a MDD zai girmama dokokin kasa da kasa ba irin yadda Nickey Haley din ta kasance.

A jiya ne dai tsohuwar jakadiyar Amurkan ta sanar da murabus dinta daga mukamin sakamakon sabanin da ta samu da shugaban Amurkan Donald Trump kamar yadda wasu majiyoyi suka fadi


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky