Amurkawa Sun Yi Zanga-Zangar Kin Amincewa Da Kai Wa Kasar Syria Hari

Amurkawa Sun Yi Zanga-Zangar Kin Amincewa Da Kai Wa Kasar Syria Hari

Dubban Amurkawa sun yi gangami da zanga-zangar yin Allawadai da ta salon siyasar ina da yaki da Donald Trump wadda ta kai shi ga kaddamar da hari a kan kasar Syria saboda dalilai na siyasa.

Tashar talabijin ta Press TV daga birnin New York ta bayar da rahoton cewa, an gudanar da wannan jerin gwano a birane daban-daban na kasar Amurka, da suka hada da Washington, New York, Los Angeles, Filadelfia da sauransu.

Masu zanga-zangar sun karba kiran kungiyoyin farar hula ne masu adawa da siyasar yaki irin ta gwamnatin Amurka, inda a birnin New York Amurkawa da dama suka yi cincirindo a gaban babban ginin Trump Power mallakin shugaban kasar ta Amurka, inda suke la'antar siyasarsa, tare da yin tir da Allawadai da harin da ya kaddamar a kan kasar Syria, inda suke cewa ba da sunansu ba.

Wasu daga cikin 'yan majalisar dokokin Amurka sun bukaci da aikewa Trump da ya bayyana a gaban majaliasr domin ya yi mata karin bayani kan dalilain kai hari Syria ba tare da izinin majalisa ba.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky