Amurka Ta Gargadi Rasha, China Da Iran Kada Su Yi Katsalanda A Cikin Zaben Kasar

Amurka Ta Gargadi Rasha, China Da Iran Kada Su Yi Katsalanda A Cikin Zaben Kasar

Gwamnatin kasar Amurka ta gargadi kasashen waje, musamman Rasha, China da kuma Iran, kan katsalandi a cikin zaben tsakiyar zango wanda za'a gudanar a yau Talata.

Jami'an tsaro a kasar Amurka sun yi wannan gargadin ne a yau Talata a dai-dai lokacin da ake shirin fara zaben tsakiyar zango a yau Talata. A Zaben na yau ne ake saran za'a zabi wakilai 435 na majalisar wakilan kasar daga jihohin 50 na kasar. Sannan za'a zabi sanatoci 35 cikin sanatoci 100 da majalisar dattawan kasar take da su. Banda haka za'a zabi gwamnoni a jihohi 36 na kasar. 

Hukumomin tsaro wadanda suka hada da banagren tsaron cikin gida, DHS, bangaren sharia DOJ da kuma bangaren yansandan ciki wato DNI. Shuwagabannin wadannan hukumomi sun bayyana cewa sun dauki shekaru 2 cur suna shirye-shiryen yadda za'a gudanar da wannan zaben cikin zaman nlafiya da adalci.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky