Amurka : Mai Yiwa Mun Hallaka Kwamandan IS Na Afganistan

Amurka : Mai Yiwa Mun Hallaka Kwamandan IS Na Afganistan

Ma'aikatar tsaron Amurka ta ce wata killah babban kwamandan kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh a Afganistan, Abdul Hasib ya hallaka a harin baya bayan nan data kai a gabashin kasar.

Sojojin Amurka da dama ne hadin gwiwa dana Afganistan suka kai samame a mabuyar ta Hasib dake lardin Nangarhar, inda kuma suka hallaka kimanin 35 daga cikin 'yan ta'addan.

Wasu majoyoyin a ma'aitakar ta Pantagon sun ce mai yiwa Hasib ya hallaka a samamen sojojin a ranr Laraba saidai ba tare da yin karin haske ba.

Idan dai har mutuwar ya tabbata Hasib ta tabbata hakan zai kasance babban koma baya ga ayyukan kungiyar ta IS a Afganistan da kuma yunkurinmu na ganin bayanta a cikin shakara 2017 a cewar babban kwamandan dakarun Amurka a Afaganistan.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky