Zimbabwe : Mnangagwa Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa

Zimbabwe : Mnangagwa Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa

Hukumar Zaben Zimbabwe ta bayyana Emmerson Mnangagwa a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar.

A daren jiya alhamis ne hukumar zaben kasar Zimbabwe ta sanar da cewa Shugaba Emmerson Mnangagwa ya lashe zaben shugabancin kasar da kashi 50.8 na kuru'un da aka kada, yayin da abokin hamayarsa Nelson Chamisa ya samu kashi 44.3 cikin dari, to saidai Mista Chamisa ya ce zai kalubalnci sakamakon da hukumar zaben ta bayyana.

Hukumar zaben ta ce Mnangagwa ya lashe shida daga cikin larduna goma da ke kasar, yayin da Nelson Chamisa na jamiyyar adawa ta MDC ya lashe larduna 4.

'Yan sanda sun fitar da jami'an yan adawa daga cikin dakin tattara sakamakon zabe lokacin da suka ki amincewa da sakamakon.

Duk da cewa an gudanar da zaben na ranar 30 ga watan yulin da ya gabata cikin lumana, to saidai zanga-zangar da aka yi na kin amincewa da sakamakon zabe ta janyo asarar rayuka a kasar.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky