Taron kasashen duniya masu karfin tattalin arziki G7

Taron kasashen duniya masu karfin tattalin arziki G7

An gayyaci wasu shugabannin kasashen Afirka domin halartar taron kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya wato G7.

Taron wanda zai share tsawon yini biyu ana gudanar da shi a Taormina da ke yankin Sicile na kasar Italiya, kamar yadda aka saba zai hada shugabannin kasashe 7 da suka fi karfin tattalin arziki a duniya, wato Amurka, Canada, Birtaniya, Faransa, Jamus, Italiya da kuma Japan.

Wannan dai zai kasance karo na farko da shugaban Amurka Donald Trump da kuma Emmanuel Macron na Faransa za su halarci taron, yayin da aka gayyaci shugabanni daga wasu kasashen nahiyar Afirka, wata dama a gare su domin gabatar da wasu daga cikin bukatun nahiyar ga manyan kasashen na duniya.

Shugban Kenya Uhuru Kenyatta, da mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo, da Firaministan Habasha Haile Mariam Dessalegn, shugaban Nijar Issoufou Mahamadou da kuma takwaransa na Tunisia Beji Caidi Essebbsi ne aka gayyata daga nahiyar Afirka.

Batun tsaro da kuma fada da ayyukan ta’addanci dai su ne muhimman batutuwan da ake kyautata zaton cewa za su fi mamaye taron na bana, lura da irin matsalolin da duniya ke fuskanta sakamakon yawaitar hare-haren ta’addanci a wannan zamani.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni