Sojojin Masar Sun Hallaka Kwamandan 'yan Ta'addar ISIS

Sojojin Masar Sun Hallaka Kwamandan 'yan Ta'addar ISIS

Dakarun Tsaron Masar sun sanar da hallaka wani kwamandan 'yan ta'addar ISIS a Tsbirin Sinai.

Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto majiyar tsaron Masar na cewa a jiya lahadi, dakarun tsaron kasar sun samu nasarar hallaka Abu ja'afar Mukaddisi daya daga cikin kwamondojin kungiyar ta'addanci ta ISIS a kauyen Shaidu-Zawid na jihar Tsibirin Sinai kusa da kan iyakar kasar da yankin Zirin Gaza na Palastinu.

A nata bangare kungiyar ISIS ta tabbatar da hallakar Abu Ja'afar Mukaddisi a wata sanarwa da suka fitar a shafinta na yanar gizo, saidai ba tayi  karin haske ba kan yadda aka kashe shin.

Tun daga watan Favrayun shekarar da ta gabata ce, dakarun tsaron Masar suka kadamar da farmaki, ta kasa, sama da ruwa a garinruwan dake jihar Tsibirin Sinai na kasar da nufin kawo karshen kungiyoyin 'yan ta'adda.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky