?>

Rushe wuraren bauta kaman Husainiyyar Baqiyyatullah yana cikin laifukan yaki _____Inji Ibrahim Musa

Rushe wuraren bauta kaman Husainiyyar Baqiyyatullah yana cikin laifukan yaki   _____Inji Ibrahim Musa

Shugaban dandamalin yada labarai na Harkar Musulunci a Nigeriya,Ibrahim Musa a wata takarda da ya aika ma manema labarai ta hanyar Skype,ya bayyana cewa rushe wuraren bauta kaman Husainiyyar dake Zariya yana cikin laifukan yaki.

A ranar Alhamis 20 ga watan Yuli ne,aka kawo ma’aikata tare da kariyar sojoji domin gina filin da aka rusa na Husainiyyar Zariya wadda mallakin Harkan Musulunci a Nigeriya ne.
Ibrahim Musa ya bayyana rashin amincewar su dangane da yunkurin gwamnatin tarayya na kwace masu wannan fili na Husainiyya wanda sojoji tare da hadin gwiwar  gwamnati jihar Kaduna suka rusa a Disambar 2015.
Ya kara da cewa bayan an binciki hukumar KASUPDA da jami’anta dangane da wannan aiki da ake yi a filin na Husainiyyar sai suka tabbatar da basu da masaniyar wannan aiki a filin.Wannan ya sanya suke zargin gwamnatin tarayya ce ta sanya ake wannan aiki a filin na Husainiyya.
Ibrahim Musa yayi kira ga mutane da kungiyoyi na duniya da cewa wannan fili da aka gina Husainiyya sun same shi ne ta halastacciyar hanya,kuma suna da dukkan takardun da suke tabbatar da wajen nasu ne.Saboda haka gwamnatin tarayya bata da hakkin ta yi gini a wajen da ba na ta ba.Kuma wannan kutse ne a filin wani saboda har yanzu fili yana matsayin nasu ne duk da an rusa masu gini in ji Ibrahim Musa.
A karshe Ibrahim Musa ya bayyana cewa:
“Babu wata hanya da za a bi domin a bamu tsoro.Kuma zamu cigaba da neman hakkokinmu da tsarin mulki ya tanadar,da cigaba da muzaharori na lumana kaman yanda aka sanmu.
“A lokaci guda muna kara jaddada kiran mu da neman a saki jagoranmu Sheikh Zakzaky tare da mai dakinsa cikin gaggawa ba tare da wani sharadi ba.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*