MDD Ta Yi Allah Wadai Da Kashe Ma'aikatan Agaji Da Mayakan Boko Haram Suka yi A Nigeriya

MDD Ta Yi Allah Wadai Da Kashe Ma'aikatan Agaji Da Mayakan  Boko Haram Suka yi A Nigeriya

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi tofin Allah tsine kan harin da kungiyar Boko Haram ta kai garin Rann na jihar Borno a tarayyar Nigeriya tare da kashe ma'aikatan bada agaji.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi Allah wadai da harin ta'addancin da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai kan garin Rann da ke karamar hukumar Kala Balge a jihar Bornon Nigeriya, inda suka kashe fararen hula ciki har da ma'aikatan bada agaji guda hudu tare da jikkata wani guda na daban.

A ranar Alhamis da almuru ne wasu gungun 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram suka kaddamar da harin wuce gona da iri kan garin Rann da ke karamar hukumar Kala Balge a jihar Borno da ke shiyar arewa maso gabashin Nigeriya, inda suka bude wuta kan jama'ar garin lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 11 ciki har da ma'aikatan bada agaji guda 4, tare da tarwatsa al'ummar garin, inda mutane fiye da 55,000 suka tsere daga muhallinsu.  


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky