Lawan Daura: Abinda Ya Sa Na Bada Umurnin A Yi Wa Majalisar Dokokin Kasar Kawanya

Lawan Daura: Abinda Ya Sa Na Bada Umurnin A Yi Wa Majalisar Dokokin Kasar Kawanya

Tsohon shugaban hukumar yansandan ciki Lawal Daura ya tabbatar da cewa shi ne ya bada umurni ga jami'an tsaro da ke karkashinsa yiwa majalisar dokokin kasar kawanya a cikin makon da ya gabata.

Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta bayyana cewa Lawal Daura ya bayyana haka ne a cikin rahoton bincike na farko dangane da wannan batun wanda Spetan yansanda Idris Ibrahim  ya mikawa mukaddashin shugaban kasa Prof. Yeme Osinbajo a jiya jumma'a.

A cikin rahoton Daura ya bayyana cewa ya yi haka ne don ya sami rahoton sirri na cewa ana son a shigi da makamai da wasu abubuwa na aikata laifi a zuwa cikin majalisar.

Rahoton wanda Daily Trust ya sami ganinsa ya kara da cewa tsohon shugaban na DSS bai fadawa mukaddashin shugaban kasa wannan batun ba kafin ya aika da jami'an tsaron da ke karkashinsa. Haka nan bai shaidawa sauran hukumomin tsaro kan batun ba kafin ya dau wannan matakin.

Rahoton ya kammala da cewa da wuya a amince da wannan dalilin don jami'an tsaron da Daura ya aika zuwa majalisar dokokin a ranar Talatan da ta gabata ba wadanda suke da korewa kan gano makamai ko da abubuwan facewa bane.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Shahadar Kwamandojin Musukunci. Haj,Kasim Sulemani Da Abu Mahdi
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni