Kungiyar Yan'uwa Musulmi Na Kasar Masar A Shirye Take Ta Shiga Tattaunawa Da Gwamnati

Kungiyar Yan'uwa Musulmi Na Kasar Masar A Shirye Take Ta Shiga Tattaunawa Da Gwamnati

Mataimakin shugaban kungiyar Yan'uwa musulmi ta kasar Masar wanda ya bukaci tattaunawa da gwamnatin kasar tare da wasu sharudda guda ukku.

Kamfanin dillancin labaran anatoli ya nakalto Ibrahim Munir yana fadar haka a jiya daren lahadi. Ya kuma kara da cewa sharuddan kungiyar sun hada da tattaunawa da jami'an gwamnatin kasar Masar kai tsaye, sake tsohon shugaban kasar Mohammad Mursi daga gidan kaso, da kuma sakin dukkan fursinonin siyasa da gwamnati take tsare da su.

Mataimakin shugaban kungiyar ta Yan Uwa musulmi ya bayyana cewa kungiyarsa bata amince da shugabancin Abdulfata sisiba don bata zo bisa ka'ida ba.

A shekara ta 2013 ne sojojin kasar Masar suka kifar da gwamnatin Mohammad Mursi bayan da rikici ya game kasar a bangarori daban daban na rayuwar mutanen kasar.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky