Kalaman TY Danjuma sun haifar da cece-kuce a Najeriya

Kalaman TY Danjuma sun haifar da cece-kuce a Najeriya

Gwamnatin Najeriya da rundunar sojin kasar sun musanta zargin da tsohon hafsan sojin kasar, Laftanar Janar Theophilus Yakubu Danjuma ya yi, in da ya ce, jami’an tsaro na hada kai da 'yan bindiga wajen kashe mutane a sassan kasar da suka hada da jihohin da ke fama da rikicin manoma da makiyaya, yayin da kuma ya bukaci jama'a da su tashi tsaye wajen kare rayukansu ko kuma a kashe su daya bayan daya.

Mr. Danjuma ya yi kalaman ne a yayin gabatar da jawabi a gaban dandazon mutanen da suka halarci  bikin yaye daliban Jami’ar Jihar Gwamnatin Taraba a karshen mako, in da yake cewa "dole ne kowannenmu ya tashi tsaye, domin sojoji ba sa cikin ‘yan baruwanmu, suna hada kai da ‘yan bindiga, suna kashe mutane, suna kashe ‘yan Najeriya, sojojin na taimaka wa zirga-zirgar ‘yan bindigar, matukar dai kuna dogaro da sojojin don ganin sun kawo karshen kashe-kashe, to dukkaninku za ku rasa rayukanku daya-bayan daya."

Kalaman na TY Danjuma sun haifar da cece-kuce a sassan Najeriya tare da jefa fargaba a zukatan wasu musamman mazauna yankin da ake fama da tashin hankali, yayin da rundunar sojin kasar ta bayyana kalaman a matsayin mara kan gado ganin cewa ya yi furucin ne a dai dai lokacin da ake ci gaba da fama da barazanar tsaro a jihohin da ke fama da rikicin manoma da makiyaya har ma da na Boko Haram.

Ministan Tsaron Kasar, Mansur Dan Ali  ya bayyana jawabin tsohon hafsan a matsayin tayar da zaune tsaye, kuma ya ce, sojin Najeriya na da kwarewa wajen gudanar d ayyukansu kamar yadda dokoki suka tanada.

Shi ma Kakakin sojin Najeriya, Birgediya Janar Texas Chukwu ya ce , abin takaici ne irin wadannan kalamai a dai dai lokacin da sojojin ke rasa rayukansu wajen kare lafiyar jama’a.

Rundunar sojin kasar dai ta bukaci al’ummar Taraba da su bi doka da oda domin kuwa duk wanda aka kama dauke da makamai ba bisa ka’ida ba, to za a hukunta shi kamar yadda doka ta ce.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky