Faransa zata gana da kasashen Nijar da Algeria kan tsaro

Faransa zata gana da kasashen Nijar da Algeria kan tsaro

A yau Laraba ministan cikin gidan Faransa, Gerard Collomb zai fara ziyarar aiki a kasashen Algeria da Nijar, inda zai tattauna da hukumomin kasar kan yaki da ta’addanci da kuma matsalar bakin haure.

Sanarwar ta ce, a Jamhuriyar Nijar, Ministan zai halarci taro kan yadda za’a magance matsalar safarar bakin-haure, wanda zai samu halartar wakilai daga kasashen Chadi, Mali, Burkina Faso, Mauritania da kuma kasar Cote d’Ivoire.

Sauran kasashen da zasu halarci taron sun hada da Guinea, Senegal da Libya, tare kuma da wakilan kasashen Jamus, Italia da Spain.

A baya bayan nan dai kasashe nahiyar Africa da ke yankin Sahel da suka hada da Nijar, Mali da kuma Burkina Faso sun fuskanci hare-haren ta’addanci, a dai dai lokacin da ayyukan rundunar dakarun hadin gwiwa na G5 Sahel suka fara kankama domin yakar ta’addanci.

Daya daga cikin hare-haren da aka kai mafi muni a baya-bayan nan shi ne na birnin Ouagadugou, inda aka kai hare-haren kunar bakin wake kan hedikwatar sojin kasar da kuma ofishin jakadancin Faransa.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky