Buhari Ya Zama Sabon Shugaban Kungiyar ECOWAS

Buhari Ya Zama Sabon Shugaban Kungiyar ECOWAS

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya karbi shugancin karba-karba na kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika CEDEAO / ECOWAS, bayan taron kungiyar karo na 53 da ya gudana a birnin Lome na kasar Togo

Shugaban kasar Togo ne, Faure Gnassingbe ke rike da shugabancin kungiyar kafin ya mika shi ga takwaransa na Najeriyar Muhammadu Buhari.

Mista Gnassingbe, ya taya Buhari murna akan zabensa a wannan matsayi tare kuma da yi masa fatan alhairi da sunan al'ummar kasar ta Togo.

Taron dai na Togo ya maida hankali kan batutuwa da dama ciki har da halin da ake ciki na rikicin siyasa a kasar ta Togo.

An dai fitar da shawarwari da dama da ake ganin zasu kai ga shawo kan rikicin siyasar na kasar ta Togo, ciki har da shirya zaben 'yan majalisar dokoki, da kuma takaita wa'adin mulki sau biyu kacal. 


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky