AN BAWA HAMMATA ISKA A TARON APC A ABUJA:

AN BAWA HAMMATA ISKA A TARON APC A ABUJA:

AN BAWA HAMMATA ISKA A TARON APC A ABUJA:


Daga Aliyu Muhammad,kaduna

A jiya ne aka gudanar da babban taron da  Jam'iyyar APC ta ke yi a  babban birnin tarayyah Abuja na zaben shuwagaban nin ta na kasa, amma wata ga garumar  rigima ta barke a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar, inda aka yi ta bawa hammata iska, anyi ta jefe jefe da kujeru,  hakan ya kawo wasu daga cikin 'ya 'yan jam'iyar ta APC jin mugayen raunuka.

 
  Rigimar ta kaure ne a inda wasu daga cikin 'ya 'yan jam'iyyar ta APC suka fusata na ganin cewa anyi musu ha'inci da maguɗi a wajen zaɓen da aka gudanar a zaben shuwagaban nin na kasa da aka gudanar a birnin na Abuja.

taron dai ya tashi baran baran, wasu kuma daga cikin 'yan  jam'iyyar suna ganin yaushe ne za'a dinke irin wannan baraka da ke cikin jami'iyyar ganin ana harar babban zabe, wasu kuma suna ganin akwai katon aiki a gaban sabon shugaban da aka zaba Mr. Adams oshimohle na dinke wannan baraka da taki ci taki cinyewa cikin jam'iyar mai mulki ta APC. 

Ko, yaya kuke kallon irin wannan baraka da ta dabaibaye jam'iyar ta APC?


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky