?>

Kuwait Tana Shirin Hana Wasu 'Yan Kasashe Shiga Cikin Kasarta

Kuwait Tana Shirin Hana Wasu 'Yan Kasashe Shiga Cikin Kasarta

Gwamnatin Kuwait tana shirin hana takardar izinin shiga kasarta ga ‘yan kasashe 10 mafi yawansu ‘yan nahiyar Afirka

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Jaridar Al-Qabas ta kasar Kuwait a yau Lahadi ta buga labarin cewa: Ma’aikatar harkokin wajen kasar tana tattauna shawarar yiwuwar hana bada takardar izinin shiga cikin kasarta “Visa” ga wasu ‘yan kasashen waje mafi yawansu ‘yan Afirka da suka hada da Madagascar, Kamaru, Ivory Coast, Ghana, Benin, Mali, Congo da wasu kasashen uku da ba na Afirka ba.

Wata majiya ta bayyana cewa: Dalilin da ya sanya bijiro da wannan batu shi ne rashin ofisoshin jakadancin gwamnatocin kasashen a kasar Kuwait, kuma ‘yan kasashen da aka kiyasta cewa sun kai dubbai a cikin kasar Kuwait, ana shirin korarsu ne saboda suna zama a kasar ce ba a kan ka’ida ba, ko wadanda kotu ta zartar musu da hukunci kan laifuka daban-daban da suka hada da safarar miyagun kwayoyi, sayar da barasa da ayyukan da suka saba wa tsarin tarbiyyar zamantakewa.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*