ALKUR’ANI BA RUWANSHI DA WANI WAI NAKA SAI NAKA

ALKUR’ANI BA RUWANSHI DA WANI WAI NAKA SAI NAKA

ALKUR’ANI BA RUWANSHI DA WANI WAI NAKA SAI NAKA
__ Cewar Sheikh Halliru Maraya

A karatun tafsirin Alkur’ani cikin suratul Yasin wanda Sheikh Halliru Maraya ya gabatar a Zawiyyar Sheikh Salihu Musa Malami Tudun Nufawa Kaduna  a ranar Alhamis, 24/5/2018, a lokacin da yake tafsiri karkashin aya YA LAITA QAUMI YA’ALAMUN inda yake bayar da kissar Habibun Najjari.
Malamin yace shi Habibun Najjari ya kasance yana ma mutanensa uzuri duk da abubuwan da suka yi masa. Sannan a cikin kissar akwai darasin koda mutum makiyinka ne kayi mai fatan alheri saboda a lokacin da Habibun Najjar ya ga ni’imomi da girma da Allah ya bashi sai yake cewa ina ma dai da mutane na zasu san dalilin abinda nayi Allah yayi min gafara? Me yayi? Shine ya kadaita Allah da tsayuwa a kan hanyar Allah.
A lokacin da malamin yake Magana akan kan riko da gaskiya da adalci sai yace:
 “ Mutum na tafka shirme sai a ce ai naka sai naka, to, Kur’ani ba ruwanshi da wani naka sai naka. Anyi wani Shugaban Kasa a nan Afrika ya fito daga wani bangare, mutanen bangaren sana’arsu in sun ga ana gwanjo suke shigo da gwanjo. Suna sana’ar motoci, suke shigo da shinkafa a kasar tasu, suke canjin kudi. Da dan wurinsu ya samu mulki ya karya gwanjon, ya karya sai da motocin, ya karya shigo da shinkafan, ya karya yan canji. Duk manyan sana’ar bangaren da ya fito sai da ya karya. Mu Nijeriya mun gode ma Allah bamu samu wannan ba. Mu Nijeriya namu ya habaka gwanjo, ya habaka shigo da shinkafa, ya habaka canji, ya habaka sai da motoci, duk sana’ar da mutanen mu suke yi ya habaka ta. Mun gode ma Allah da bai mana irin na wayancan ba. Ka ga mu a wurin namu ka ga namu sai namu ne ai ko? Tunda ya habaka sana’o’inmu.
 “ Saboda haka ko yaushe abinda ya kamata ka duba shine wanene yake da gaskiya, ba wai bangare ba. In an je Lahira Ubangiji ba zai ce ina ‘yan Arewa ba? Kuyi nan. Ina ‘yan Kudu? Ina! Ina masu gaskiya? A ranar babu wani kudu babu Nijeriya ba waye ba meye Kudu balle. A ranar gaskiya da karya ne. Jam’iyyu biyu a lahira; karya da gaskiya. Ba Kudu, ba Arewa, ba maganan musulmi, ba maganar wand aba musulmi ba sai Islam. Ba maganar muslimuna sai Islam, shine zai cece ka.
 “ Islam daban, muslim daban. Musulmi daban, musulunci daban. Duk duniya mun fi son musulunci amma akwai musulmi mutumin banza, akwai kirista mutumin banza. Akwai musulmi mutumin kirki, akwia kirista mutumin kirki. Saboda haka yayin da aka zo ka dub aka ga wanene ya bi fadan Annabi, wanene yake da halin da Annabi yake so. Wannan barawo ne musulmi. Wannan ya rike amana kirista ne. Inda Annabi zai bayyana wanene yayi hali irin na Annabi duk da bai addinin Annabi ba? Kirista. Shi yasa lokacin da ake cutar da mutane a Makkah ana kasha Sahabbai ana wa Sahabbai barazana sai Annabi yace su tafi Habasha wajen Kirista. Annabi yace a Habasha akwai wani Shugaba Kirista ne amma adili. Ba haka aka yi ba? Saboda haka kada wani ya rude ka da Arewa ko abin nan da sauransu.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni