?>

Kotun Mali Za Ta Gurfanar Da Ministan Harkokin Wajen Faransa

Kotun Mali Za Ta Gurfanar Da Ministan Harkokin Wajen Faransa

Wata babbar kotu a birnin Bamako na kasar Mali, ta nemi ministan harkokin wajen faransa, Jean-Yves Le Drian, da ya gurfana gabanta game da wata warka data shafe shi.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A wata wasika da ta fitar kotun ta bukaci Mista Le Drian, da ya gurfana gabanta a ranar 20 ga watan Yuni mai zuwa a karfe takwas.

Bayanai daga Malin, sun ce ana zargin Jean-Yves Le Drian da dansa Thomas, da hannu a aikata ba daidai ba kan dukiyoyin al’umma da kuma wasu laifuka ga kasar Mali a shekarar 2015.

A nata bangare kasar ta Faransa ta ce babu wanda ya tuntubi ofishin jakadabcinta kan batun data danganta da wata sabuwar tsokana daga Malin.

Wata kungiyar Mali ce mai suna Maliko, ta shigar da kara gaban kotun, inda ta ke zargin Jean-Yves Le Drian, a lokacin yana ministan tsaron faransa da amfani da mukaminsa wajen tursasawa tsohon shugaban kasar Ibrahim Bubakar Keita, baiwa wani kamfanin faransa na bretonne da ake kira Idemia a yau kwagila ta yin fasfon Mali, maimakon baiwa wani kamfanin Canada kwangilar.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*