?>

Korona Ta Bulla A Karon Farko A Koriya Ta Arewa

Korona Ta Bulla A Karon Farko A Koriya Ta Arewa

A sama da shekaru da gano annobar Korona a makobciyarta China, Koriya ta Arewa ta sanar da bullar annobar korona a kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Shugaban kasar Kim Jong-un, yayin wani taro kan lamarin, ya bada umarnin kafa matakan gaggawa domin dakile kwayar cutar.

Tuni aka kafa dokar killace jama’a da karfafa bincike a iyakoki a arewacin babban birnin kasar Pyongyang, inda aka gano mutum na farko da ya kamu da cutar nau’in Omicron BA.2.

Lamarin dai zai iya kasancewa babban abun damuwa ga kasar wacce bata taba gudanar da riga kafin cutar ta korona ba ga al’ummarta.

Koriya ta Arewa dai ta yi watsi da duk wani taimakon da akayi mata na alluran riga kafin cutar ta korona daga kasashen Rasha da China hatta da MDD.

A watan Satumban 2021, shugaba Kim Jong-un, ya yi fatali da tallafin riga kafin korona miliyan uku da asusun Unicef ya bai wa kasar, yana mai cewa zasu yaki cutar da dabarunsu musamman rufe kasar da kwararen matakai.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*