?>

Katar: Gwamnatin Kasar Qatar Ta Yi Allawadai Da Kissan Yar Rahoton Aljazeera A Falasdin Da Aka Mamaye

Katar: Gwamnatin Kasar Qatar Ta Yi Allawadai Da Kissan Yar Rahoton Aljazeera A Falasdin Da Aka Mamaye

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Qatar ta bayyana kissan da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka yiwa bafalasdiniya ‘yar jarida mai yiwa tashar talabijin ta “Aljazee aiki a Jenin a matsayin wani abin allwadai ne kuma cewa hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ma’aikatar ta fidda wannan bayanin ne a yau Laraba ta kuma kara da cewa alhakin mutuwar Shirin Abu Akila yana hannun sojojin HKI kuma dole ne gwamnatin yahudawan ta kawo karshen tashe-tashen hankulan da ke faruwa a yankunan falasdinawa da ta mamaye. Don kawo karshen kisan ‘yan jarida da kuma sauran Falasdinawa.

A safiyar yau Laraba ce, sojojin yahudawan suka bindige Shirin Abu Akila har lahira a lokacinda take bada rahoton irin ta’asan da sojojin yahudawan suke yi a garin Jenan na yankin yamma da kogin Jordan.

Shirin Abu Akila yar shekara 51 a duniya ta gamu da ajalinta ne saboda yada gaskiyar abinda sojojin yahudawa suke aikatawa a yankunan Falasdinawa da suka mamaye.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*