?>

Kasar Indiya Ta Hana Fitar Da Alkamarta Zuwa Ketare

Kasar Indiya Ta Hana Fitar Da Alkamarta Zuwa Ketare

Kasar Indiya ta sanar da haramta fitar da alkama daga kasar zuwa ketare, a wani mataki na dakile matsalar hauhawan farashin kayan abinci.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tunda farko dai Indiya ta yi alkawarin fitar da alkama mai yawa ga duniya domin shawo kan matsalar tsadar abinci sakamakon yakin Rasha da Ukraine.

Saidai a yanzu Indiya, ta ce za ta saida alkamar ta ne kawai a cikin gida, amma ta ce zata iya sayarwa kasashen dake cikin tsananin bukata.

Matakin na Indiya ya biyo bayan da kasar ta fuskanci zafi mai tsanani, wanda ya kawo mata cikas wajen girbar alkama a baya baya nan.

Wannan dai babban nakaso ne ga kasashen da tuni suka karkata wajen kasar ta Indiya domin cike gibin alkamar da suke yo oda.

Kasashen Masar da Turkiyya, duk sun riga sun bada odar sayen alkamar ta Indiya, a yayin da wasu kasashen Afrika da na Gabas ta tsakiya su ma suka bi sahu.

Dama dai kungoyoyin kasa da kasa da dama sun yi gargadi akan hauhawan farashin kayan abinci sakamakon rikicin Rasha da Ukraine, kasashen dake sahun gaba wajen fitar da alkama da takin gona a duniya.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*