?>

Kasar Guinea Ta Bar Iyakarta Da Mali A Bude Duk Da Takunkumin Da ECOWAS Ta Sanya Mata

Kasar Guinea Ta Bar Iyakarta Da Mali A Bude Duk Da Takunkumin Da ECOWAS Ta Sanya Mata

Kakakin Shugaban mulkin soja na kasar Guinea ya sanar cewa gwamnatin kasar za ta ci gaba da barin iyakarsu da kasar Mali Abude duk da takunkumin da kungiyar ci gaban kasashen yammacin Afrika Ecowas ta kakabawa Bamako.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Gwamnatin da Kanar Mamady Doumbouye ke jagoranta ta kalubalanci matakin da kungiyar Ecowas ta dauka ne a ranar lahadi da ta gabata inda ta kakabawa Gwamnatin Mali takunkumi na rike dukkan kudadenta dake babban bankin raya kasashen yammacin Afrika, da kuma rufe dukkan iyakokinta da sauran kasashe

A cikin wani bayani da kwamitin sasantawa da ci bagan kasar Guinea ya fitar ya nuna cewa muna faricin cikin sanar da dukkan Alummar kasa da ma na kasa da kasa cewa gwamnatin kasar Guinea bata goyon bayan matakin da kungiyar Ecowas ta dauka a taron musamman karo na 4 da ta gudanar a birnin Accra na kasar Ghana. Bayan da ta yi wasti dad a jadawalin da mali ta mika mata na mika mulki ga hannun farar hula nan da shekaru 5 masu zuwa

A martanin farko da kasar Mali ta fitar game da matakin da kungiyar ta Ecowas ta dauka a kanta ta bayyana cewa har yanzu dai kofar tattaunawa abude take tsakaninta da kungiyar ta Ecowas.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*