?>

Jerin Gwano A Afrika Ta Kudu Domin Neman Sakin Sheikh Zakzaky

Bangaren kasa da kasa, an gudanar da jerin gwano a kasar Afrika da ta kudu domin kira da a saki Sheikh Ibrahim Zakzaky

(ABNA24.com) Daruruwan jama’a ne suka gudanar da jerin gwano da gangami a kasar Afrika ta kudu, domin yin kira da a saki Sheikh Zakzaky da a ke tsare da shi a Najeriya.

Rahoton ya ce an gudanar da gangamin ne a gaban kananan ofisoshin jakadancin Najeriya da ke biranan Johannesburg da kuma Cape Town, inda masu gangamin suka yi kira ga mahkuntan Najeriya kan su saki Sheikh Zakzaky domin kula da lafiyarsa.

Wannan jerin gwano na zuwa ne bayan fitar da bayanai dangane da yanayin lafiyar Sheikh Zakzaky, inda wani sakamakon binciken liitoci ya nuna cewa yana fama da matsaloli masu hadri ga makomar lafiyarsa.

Daga ciki har da cewa an samu sanadarai mas guba a cikin jininsa bayan gwaji.
/129


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*