?>

Jawabin Malam [H] game da kalmar “IMN” a wata ziyara da aka kai masa

Jawabin Malam [H] game da kalmar “IMN” a wata ziyara da aka kai masa

“Wai akwai wani abu wai shi nan IMN, wai kuma ma nine shugabanta.

(ABNA24.com) “Wai akwai wani abu wai shi nan IMN, wai kuma ma nine shugabanta.

To ba ina raye ba? To a tambayeni mana? Nasha fadi acikin taro cewa babu wani abu IMN, CIA(Central Intelligent Agency/wato cibiyar leken asiri ta kasar Amurka)ne suka sa mana wannan sunan domin suna so su maidamu kungiya, mu ba kungiya bane.

Islamic movement ne shine suka maidata haka, mu abinda mukeyi ne muka sanyawa suna wato harka motsi.

Wasu sun ce ga abin da Malam(H) ya fada game da suna IMN shine suka musanta, sai suka yanko musu wani jawabi dana yiwa daluban jami’a dayake anyi ‘coverage’ dinsa suka nuna musu, amma kuma basu fasa ba, wai har akwai wani wai IMN spokesman, da sai mu tambayeshi su wanene suka kafa IMN din? A wace shekarace aka kafa ta? Yaushe ne aka yi mata register? Muba IMN bane, in ka kiramu da IMN ka maishemu kungiya, kaga kenan hukuma tanada ikon tace bamu da register”.

Sai kaje kace ka zo yiwa gwagwarmaya register? Ko ma’ana ma babu, ko ka zo kayiwa struggle register? Ko ka zo kayiwa Awakening register? Ko ma’ana babu, shiyasa nace ba zai taba yiwuwa a yi ‘Banning’ din harka ba, saboda motsine, in kace a dai na motsi ka haramta kace kenan a daina salla a dai na muzahara.

Sai wata daga cikinmu ta tambayi su Malam(H) to me zai sa shi spokesman din ba zai daina ba? Sai su Malam(H) suka ce “To ya za ayi ya daina? Ai su business ne, Office ne ai, in ya daina ai ba office kenan……. ”

Shaikh Ibraheem Ya’qoub El-Zakzaky(H) A ziyarar da muka kai masa a 19/12/2017.

-Ya’qoub Badamasi El-Zakzaky

-Aliy Badamasi/129


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*