?>

Janar Mousavi: Kan Iyakan Iran Da Afghanistan Na Cikin Aminci, Sojoji Na Ci Gaba Da Sanya Ido

Janar Mousavi: Kan Iyakan Iran Da Afghanistan Na Cikin Aminci, Sojoji Na Ci Gaba Da Sanya Ido

Babban hafsan hafsoshin ƙasa na Iran ya bayyana cewar abin da ke faruwa a halin yanzu a Afghanistan bai zama wata barazana ga tsaron kan iyakokin Iran ba don kuwa sojoji da sauran jami’an tsaron Iran suna ci gaba da sanya ido a kan iyakokin.

ABNA24 : Babban hafsan hafsoshin sojojin na Iran, Manjo Janar Abdolrahim Mousavi ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da yayi da manema labarai a yayin wata ziyara da ya kai kan iyakan Dowqarun da ke kudu maso gabashin ƙasar ta Iran don gane wa idanuwansa halin da ake ciki a can, inda ya ce:

“Dakarun ƙasarmu suna cikin yanayi mai kyau kamar yadda shekara da shekaru kenan suke shirin fuskantar duk wata barazana. Don haka abin da a halin yanzu yake faruwa a Afghanistan koda wasa ba zai zama barazana ga Iran ba”.

Babban hafsan hafsoshin sojin ƙasa na Iran ɗin ya ce sama da kashin 90 cikin ɗari na kan iyakokin Iran ɗin suna ƙarƙashin sa idon dakarun na Iran ta hanyar amfani da na’urorin zamani.

Shi ma a nasa ɓangaren babban kwamandan sojojin ƙasa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na ƙasar ta Iran Birgediya Janar Mohammad Pakpour ya ce komai yana tafiya kamar yadda ya kamata a kan iyakan ƙasar ta gabas da ƙasar Afghanistan inda a halin yanzu ake fama da rikici tsakanin dakarun gwamnati da na ƙungiyar Taliban.

Cikin ‘yan kwanakin nan dai rikici ya barke tsakanin dakarun gwamnatin Afghanistan da dakarun ƙungiyar Taliban sakamakon janyewar da dakarun Amurka suka yi daga ƙasar inda Taliban ɗin take ci gaba da ƙwace yankuna daban-daban na ƙasar wanda ake ganin hakan a matsayin barazana ga ƙasar da ma ƙasashen da suke makwabtaka da ita.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*