?>

Jam’iyya Mai Mulki A Kasar Rasha Ta Sanar Da Nasarar Lashe Zaben Majalisar Dokokin kasar

Jam’iyya Mai Mulki A Kasar Rasha Ta Sanar Da Nasarar Lashe Zaben Majalisar Dokokin kasar

Rahotanni dake fitowa daga kasar Rasha sun bayyana cewa Jami’iyar United Russia Party da ke samun goyon bayan shugaban kasar Viladmir Putin ta ci gaba da rike rinjayen da take da shi a majalisar bayan zaben majalisar dokokin da aka gudanar , inda ta lashe aksarin kujerun majalisar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Hukumar zabe ta sanar cewa bayan kirga kuri’u kashi 64% Jam’iyar United Russia ta lashe kusan kashi 48 cikin dari na dukkan Kuri’un da aka kada inda abokiyar hammayarta wato Jam’iyar gurguzu ta samu kashi 21% na dukkan kuri’un ,

Yanzu haka dai sakamakon da aka fitar ya nuna cewa Jam’iyar gurguzu ita ce ta zo ta biyu sai kuma Jam’iyar LDPR ke bi mata da ta samu kashi 8, sai kuma Fair Russia Party kuma ta samu kashe 7, sai kuma wata sabuwar Jam’iyya da ta fito mai suna New people ta samu kashi 6 cikin dari na kujerar majalisar.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*