?>

Jakadan Amurka A Rikicin Yamen Ya Ce Iran Zata Taimaka Wajen Dawo Da Zaman Lafiya A Yemen

Jakadan Amurka A Rikicin Yamen Ya Ce Iran Zata Taimaka Wajen Dawo Da Zaman Lafiya A Yemen

Manzon kasar Amurka na musamman kan rikicin kasar Yeman Mr Timothy Lenderking ya bayyana cewa kasar Iran tana da gagarumin rawan da zata taka wajen dawo da zaman lafiya a kasar Yemen.

ABNA24 : Shafin yanar gizo na labarai mai suna ‘Hail” ya nakalto Landerking yana fadar haka a yau Laraba, a ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Amurka.

Wannan jami’an diblomasiyyar kasar ta Amurka ya burus ta mummunan halin da mutanen kasar Yemen suke cikin saboda killacewa da kuma hare-haren da saudiya da kawayenta suke kaiwa kan mutanen kasar ta Yemen, sannan ya tuhumi kasar Iran da tallafawa kungiyar Ansarallah da horaswa da kuma makamai.

Tun ranar 15 ga watan Maris na shekara ta 2015 ne kasashen saudiya da UAE da wasu kawayensu suka farwa kasar Yemen da yaki da nufin maida tsohon shugaban kasar Abdu rabbu Mansur Hadi kan kujerar shugabancin kasar.

A halin yanzu an shega shekara ta 7 kenan ba tare da sun cimma wannan burin ba.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni