?>

Jagora: Makiyan Iran Da Musulunci Suna Yakarsu Ne Ta Hanyar Dabarar Lallaba

Jagora: Makiyan Iran Da Musulunci Suna Yakarsu Ne Ta Hanyar Dabarar Lallaba

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa: Makiyan Iran da Musulunci sun koma yakarsu ne ta hanyar dabarar lallaba.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A jawabin da ya gabatar yayin ganawa da jami’an kwamitin babban taron kasa don girmama shahidan kabilun Iran a yau Talata: Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullahi Uzmah Sayyid Ali Khamene’i ya yi nuni da kalaman marigayi Imam Khomeini {r.a} cewa; ‘Ya’yan kabilu suna matsayin arziki ne ga kasa, don haka hanyar kubutar da kai daga makircin makiya yana ga matakin da al’ummar kasa ta dauka na yin riko da al’adunta musamman kabilu.

Jagoran yana mai fayyace cewa: Makiya sun so yin tasiri kan kabilun Iran da nufin juyar da akalarsu zuwa ha’intar kasa da janyo rarraba a tsakanin al’ummar Iran sannan kunna wutar rikicin kabilanci amma hakarsu ba ta kai ga ruwa ba.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*