?>

Jagora: Dole Ne Yan Makaranta Su Fahinci Muhimman Zama Dan Kasa

Jagoran juyin juya halin Musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa tsarin karatu na shekaru 12 a kasar Iran wada babbar dama ce tarbiyantar da yan kasar kan abubuwan da yakamata su sani ilmin rayuwa a kasar Iran.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a safiyar yau laraba a lokacinda yake gana da zababun daliban jami’o’ii a gidansa dake nan Tehran.

Imam Khaminae ya godewa malaman makarantu da irin kokarin da suke baje a lokacin da cutar korona ta yadu a kasar shekaru 2 da suka gabata.

A wani bangare jagoran ya bukaci malaman makarantu daga firaimari har jami’i’o’ii, su sanar da dalibansu tarihin juyin juya halin musulunci da kuma yadda duniyar take tafiya a halin yanzu don su koyi juriya da kuam sannan yadda zasu fuskanci makiya.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*