?>

Ivory Coast: Shugaba Ouattara Ya Gana Da Laurent Gbagbo A Karon Farko Cikin Shekaru 10

Ivory Coast: Shugaba Ouattara Ya Gana Da Laurent Gbagbo A Karon Farko Cikin Shekaru 10

Shugaban ƙasar Ivory Coast Alassane Ouattara yayi alƙawari aiki tare da tsohon shugaban ƙasar Laurent Gbagbo wajen tabbatar da kwanciyar hankali da zaman lafiya don ciyar da ƙasar gaba.

ABNA24 : Shugaba Ouattara ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da tsohon shugaban ƙasar Laurent Gbagbo wanda ya kai masa ziyara fadarsa da ke birnin Abidjan a jiya Talata, wanda ita ce ganawa ta farko tsakanin shugabannin biyu cikin shekaru 10 tun bayan ɓarkewar rikicin da yayi sanadiyyar mutuwar wani adadi mai yawa na mutanen ƙasar a shekara ta 2010-2011.

A wata ganawa da haɗin gwuiwa da manema labarai da shugabannin biyu suka yi bayan ganawar da suka yi a tsakaninsu, shugaba Ouattara ya ce: ‘rikici na haifar da saɓani, to amma a halin yanzu komai ya wuce. Abin da ke da muhimmanci shi ne tabbatar da zaman lafiya a ƙasar mu”.

Shi ma a nasa ɓangaren tsohon shugaba Gbagbo ya buƙaci da a sako mutanen da ake tsare da su sakamakon rikicin da ya ɓarke a ƙasar biyo bayan ƙin amincewarsa da kayen da ya sha a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar.

Rikicin dai yayi sanadiyyar mutuwar sama da mutane 3000 a ƙasar kana kuma hakan ne ya sanya aka miƙa tsohon shugaba Gbagbo ɗin kotun duniyar mai shari’ar manyan laifuffukan yaƙi saboda tuhumar da ake masa cikin haddasa rikicin sai dai bayan shari’a na shekaru kotun ta wanke shi inda ya dawo gida Ivory Coast ɗin a watan da ya gabata.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*