?>

Isma’il Haniyyah Ya Yi Kira Kan Samar Da Kawancen ‘Yantar da Masallacin Aksa

Isma’il Haniyyah Ya Yi Kira Kan Samar Da Kawancen ‘Yantar da Masallacin Aksa

Isma’il Haniyyah ya yi kira kan samar da wani babban kawance don ‘yantar da Masallacin Aksa da kuma gudanar da gagarumin shirin tallafawa al’ummar Falasdinu

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Shugaban ofishin bangaren siyasa ta kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta Falasdinu Isma’il Haniyya a yau Lahadi ya bayyana cewa: Hakki ne da ya rataya a wuyar al’ummar Falasdinu da ‘yantattu na duniya, goyon bayan gwagwarmayar Falasdinawa na neman hakkokinsu, yana mai jaddada cewa: Babu ja da baya a kokarin ‘yantar da gabar yammacin kogin Jordan da aka mamaye da birnin Qudus da kuma dukkanin kasar Falasdinu mai albarka.

Har ila yau Isma’il Haniyah ya jaddada rashin dacewar duk wani matakin kulla alakar jakadanci da gwamnatin Haramtacciytar kasar Isra’ila ‘yar mamaya saboda hakan zai kara mata karfin ci gaba ne da aiwatar da bakar siyasarta kan al’ummar Falasdinu na danne musu hakkokinsu.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*