?>

Iran Za Ta Rage Aiki Da Bai Wa Masu Sa-Ido Damar Ziyartar Cibiyoyinta Na Nukiliya A Duk Lokacin Da Su Ka Ga Dama

Iran Za Ta Rage Aiki Da Bai Wa Masu Sa-Ido Damar Ziyartar Cibiyoyinta Na Nukiliya A Duk Lokacin Da Su Ka Ga Dama

Mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Abbas Iraqchi ya sanar da cewa, matakin yana nufin fage bai wa masu sa ido din damar kawo ziyara ta ba-zata a duk lokacin da su ka ga dama da kaso 20 zuwa 30%.

ABNA24 : Sai dai Iraqchi ya kara da cewa; Hakan ba ya nufin cewa Iran din ta kori masu sa ido din baki daya.

Har ila yau, mataimakin ministan harkokin wajen na Iran ya ce; Kasashen turai ba su da hakkin da za su zargi Iran da jefa matakan diplomasiyya cikin hatsari.

Iraqchi ya kuma ce; Iran ta bai wa kasashen na turai dama wadatacciya, amma ba su iya hana Amurka janyewa daga cikin yarjejeniyar ta Nukiliya ba.

Bugu da kari Iraqchi ya ce da Iran tana son bude tattaunawa akan shirinta na makamai masu linzami to da ta yi da gwamantin Turmp. Don haka ba za ta yi ba a wannan lokacin.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni