?>

Iran Tana Nazarin Gayyatar Tarayyar Turai Na Hallatar Taron JCPOA Wanda Wakilin Amurka Zai Halarta

Iran Tana Nazarin Gayyatar Tarayyar Turai Na Hallatar Taron JCPOA Wanda Wakilin Amurka Zai Halarta

Matimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran tana nazarin gayyatar tarayyar Turai don halattan taron kasashe P4+1 wadanda suka samar da yarjejeniyar shirin nukliyar kasar wacce aka fi sani da JCPOA daga cikin har da wakilin kasar Amurka.

ABNA24 : Ariqchi ya kara da cewa Iran zata yi nazarin wannan bukatar tare da sauran kawayenta wadanda suka hada da Rasha da kuma Sin. Ana saran idan Iran Iran ta amince da halattan taron gwamnatin shugaban Biden na Amurka zai tura Rob Malley mai bashi shawara na musamma kan al’amuran kasar Iran zuwa Taron.

Amurka ta fice daga yarjejeniyar JCPOA a shekara ta 2018 sannan ta take dukkan dokokin kasa da kasa kan yarjejeniyar nukliyar kasar Iran, ta dora mata takunkuman tattalin arziki mafi muni a tarihin kasar.

Josep Borrell jami’ii mai kula da lamuran kasashen waje na tarayyar Turai ne ya gabatar da wannan bukatar a ziyarar da yake yi a nan birnin Tehran.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni