?>

Iran Ta Yi Tir Da Tsoma Bakin Amurka Cikin Zanga-Zangar Da Ke Gudana A Кasar Cuba

Iran Ta Yi Tir Da Tsoma Bakin Amurka Cikin Zanga-Zangar Da Ke Gudana A Кasar Cuba

Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen Iran Saeed Khatibzadeh yayi kakkausar suka ga yadda Amurka da wasu ƙasashen yammaci suke tsoma bakinsu cikin zanga-zangar baya-bayan nan da ke gudana a ƙasar Cuba, yana mai kiran Amurkan da ta daina tsoma baki cikin harkokin ƙasar.

ABNA24 : Mr. Khatibzadeh ya bayyana hakan ne a yayin da yake magana kan zanga-zangar da ke gudana a halin yanzu a ƙasar Cuban inda ya ce a daidai lokacin da Amurka ita ce ummul aba’isin ɗin mummunan halin da ƙasar Cuban take ciki, lalle abin baƙin ciki da kunya ne yadda Amurkan take nuna kan ta a matsayin mai goyon bayan al’ummar Cuba masu zanga-zangar. Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya kammala da cewa Iran a matsayinta na ƙasar da take fuskantar irin wannan takunkumi na zalunci na Amurka, tana sanar da goyon bayanta ga gwamnati da kuma al’ummar Cuban sannan kuma tana kiran da a gaggauta kawo ƙarshen takunkumin zaluncin da aka sanya mata. Cikin ‘yan kwanakin nan dai ƙasar Cuban tana fuskantar zanga-zangogin wasu daga cikin al’ummomin ƙasar sakamakon matsi na rayuwa da suke fuskanta. Shugaban ƙasar Cuban dai Diaz-Canel ya zargi Amurka da hannu cikin tashin tashi nan da ke faruwa a ƙasar.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*