Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta yi allawadai da harin ta’addancin da ya yi sanadin mutuwar sojojin Masar 11 a yankin Sinai.
Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Saeed Khatibzadeh, ya ce abun takaici ayyukan ta’addancin dake samun goyan bayan kasashen ketare na ci gaba da yaduwa a kasashen musulmi, wanda ke bukatar hadin kan kasashen yankin domin yakar ta’addancin.
A ranar Asabar ne wasu da ake zaton mayakan wata kungiyar ta’addanci ne, suka farwa rukunin sojoji Masar din dake aiki a wata cibiyar tace ruwa dake yammacin yankin Sinai, inda nan take suka hallaka sojoji a kalla 11, tare da jikkata wasu 5.
342/