?>

Iran Ta Yi Кarin Bayani Kan Gazawar Takunkumin Amurka A Kan Кasar

Iran Ta Yi Кarin Bayani Kan Gazawar Takunkumin Amurka A Kan Кasar

A yayin da ake bikin tunawa da shekaru shida da sanya hannu kan yarjejeniyar nukiliyan Iran, ministan harkokin wajen ƙasar ta Iran, Muhammad Javad Zarif yayi ƙarin bayani kan gazawar Amurka wajen cimma manufarta ta matsin lamba da sanya wa Iran takunkumi yana mai ishara da irin ci gaban da Iran ta samu a fagen fasahar nukiliya duk kuwa da takunkumin Amurkan.

ABNA24 : Ministan harkokin wajen na Iran ya bayyana hakan ne cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter don tunawa da shekaru shida da sanya hannu kan yarjejeniyar ta nukiliya da ake kira da JCPOA inda ya ce “yau shekaru 6 kenan da yarjejeniyar JCPOA ta rufe babi na 7 na ƙudurin Kwamitin Tsaron Majalisar Ɗinkin Duniya ba tare da an ƙaddamar da yaƙi ba”. Ministan harkokin wajen na Iran ya ci gaba da yin bayanin matakan da Amurka ta dinga ɗauka tun bayan da aka cimma yarjejeniyar a shekara ta 2015 yana mai cewa ta gaza wajen cimma manufarta kuma a nan gaba ma ba za ta cimma ba. Dr. Zarif yayi kakkausar suka ga siyasar Amurka ta sanya takunkumi wa ƙasashe da suka saɓa mata da ƙin amincea da siyasarta yana mai cewa lokaci yayi da Amurkan za ta yi watsi da wannan siyasa tata. Wadannan kalamai na Zarif ɗin suna zuwa ne a daidai lokacin da Iran ɗin take ci gaba da tattaunawa da manyan ƙasashen duniya kan yadda za a sake raya yarjejeniyar nukiliyan da kuma ƙoƙarin dawo da Amurka cikinta bayan ta fice a shekara ta 2018.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*