?>

Iran Ta Sake Aikewa Da Jirgin Ruwa Mai Dauke Da Makamashi Zuwa Kasar Venezuela

Iran Ta Sake Aikewa Da Jirgin Ruwa Mai Dauke Da Makamashi Zuwa Kasar Venezuela

Cibiyar da take bibiyar kai da komowar jiragen ruwa a duniya ta sanar a shafinta na “Twitter” kan cewa, Iran ta sake aikewa da jirgin ruwa dauke da makamashi zuwa kasar Venezuela.

ABNA24 : Sanarwar ta kunshi cewa; Man da Iran din ta aike zuwa yankin El-Palito da ke kasar Venezuela, ya kai lita miliya 44, wanda shi ne karo na uku da Iran take aika makamashi zuwa Venezuela ta jiragen ruwa masu daukar makamashi.

A ranar 24 ga watan Mayu na 2020 ne dai Iran din ta fara aika man fetur zuwa kasar Venezuela a karkashin rakiyar jiragen ruwa na yaki na kasar ta Venezuela.

Jirgin ruwa na biyu dauke da makamashi na Iran zuwa kasar ta Venezuela ya isa kasar ne a ranar 25 ga watan Mayu na 2020.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni