?>

Iran Ta Jajantawa Mali Game Da Hare haren Ta'addanci

Iran Ta Jajantawa Mali Game Da Hare haren Ta'addanci

Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta jajantawa kasra Mali game da jerin hare haren ta’addancin da sukayi sanadin mutuwar mutum kimanin 132 a tsakiyar kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Da yake sanar da hakan kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Saeed Khatibzadeh, ya aike da sakon ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar Malin, dama iyalan wadanda lamarin ya rusa dasu, tare da yin allawai da harin da ya yi sanadin mutuwar wadanda basu ji basu gani ba.

Kimanin fararen hula 132 ne aka kashe a hare haren da aka kai a wasu kauyuka uku dake yankin karkarar Bankass a tsakiyar Mali.

Gwamnatin Malin ta ce za ta dauki dukkan matakan da suka dace domin gano mutanen dake da hannu a hare haren tare da gurfanar da su gaban shari’a.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*