?>

Iran Ta Ce A Shirye Take Ta Aiwatar Da Musayen Fursunoni Da Amurka Da Birtaniya

Iran Ta Ce A Shirye Take Ta Aiwatar Da Musayen Fursunoni Da Amurka Da Birtaniya

Jamuriyar Musulunci ta Iran ta yi watsi da kalaman Amurka na musanta yarjejeniyar musayen fursunoni da aka cimma da ita, tana mai cewa a shirye ta ke a ci gaba da aiwatar da yarjejejeniyar musayen fursunonin da ta cimma da Amurka da Birtaniya.

ABNA24 : Kakakin Ma’aikar harkokin wajen na Iran, Saeed Khatibzadeh, ne ya bayyana hakan cikin wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na Twitter a yau Lahadi inda yayin da yake watsi da ikirarin Amurka na cewa babu wata magana ta musayen fursunoni tsakanin ɓangarori biyun ya bayyana cewar: lalle akwai yarjejeniyar da aka cimma dangane da musayen fursunoni, hatta ma da yadda za a sanar da hakan.

Khatibzadeh ya ƙara da cewa akwai yarjejeniyar fursunoni saboda dalilai na ‘yan’adamtaka da aka cimma da Amurka da kuma Birtaniyya a birnin Vienna wacce ba ta da alaƙa da yarjejeniyar nukiliya.

Kafin hakan ma dai mataimakin ministan harkokin wajen na Iran kana kuma babban jami’in ƙasar da ke tattaunawa kan yarjejeniyar nukiliya, Abbas Araqchi ya tabbatar da batun yarjejeniyar musayen fursunonin da aka cimma tsakanin Iran da Amurka da Birtaniya.

Kalaman na su dai suna zuwa ne bayan da kakakin Ma’aikatar harkokin wajen Amurka Ned Price ya musanta cimma wata yarjejeniya ta musayen fursunonin.

Wasu masana dai suna ganin Amurkan tana ƙoƙarin haɗa sake dukiyar Iran da take riƙe da su ne ba bisa ƙa’ida sakamakon takunkumin zaluncin da ta sanya wa ƙasar da batun musayen fursunonin sannan kuma ta sami damar buɗe wata sabuwar hanya ta tattaunawa da Iran kan wasu batutuwa da Iran ta ce ba na tattaunawa ba ne.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*