Shugaban hukumar Zirga-zirgar jiragen ruwa na Iran, Babak Afqahy ya bayyana cewa; Bayan da aka kammala daukar dukkanin matakan da su dace, ana shirin bude zirga-zirgar jiragen ruwa a tsakanin Iran din da kasar Afirka ta kudu, da kuma kasashen yankin Latin Amurka.
ABNA24 : Har ila yau, ya kuma ce; Jiragen ruwan na Iran za su rika tashi ne daga tashar jirgin ruwa ta Bandar Abbas da ke kudancin Iran, su kuma yada zango a tashar jiragen ruwan Afirka ta kudu, sannan su wuce zuwa kasar Brazil.
Afqahy ya kara da cewa; Bude wannan layin na Zirga-zirgar jiragen ruwa a tsakanin Iran din da kasar Afirka ta kudu da kuma Brazila zai kara bunkasa harkokin kasuwanci a tsakanin kasashen.
A cikin watanni shida na shekarar da ta gabata, yawan kudaden hada-hadar kasuwanci a tsakanin Iran da Afirka ta kudu sun kai dala miliyan 43.
342/