?>

Iran Da China Sun Sha Alwashin Kara Karfafa Alakar Dake Tsakaninsu

Iran Da China Sun Sha Alwashin Kara Karfafa Alakar Dake Tsakaninsu

Kasashen Iran da kuma China, sun sha alwashin kara karfafa alakar dake tsakaninsu.

ABNA24 : Wannan bayanin ya fito ne bayan wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin ministan harkokin wajen kasar ta Iran da kuma takwaransa na China Wang Yi.

Yayin tattaunawar, bangarorin sun tabo batun alakar dake tsakaninsu da kuma halin da ake ciki a kasar Afganistan.

Ministan harkokin wajen China, Wang Yi, ya godewa gwamnatin Hassan Rohani, kan kokarin data yi na karfafa alaka tsakanin kasashen biyu a cikin shekaru takwas.

Haka kuma Sin, ta yi fatan kara karfafa wannan alaka a karkashin sabuwar gwamnatin Ebrahim Ra’isi da zata zo nan gaba.

Shi kuwa Zarif, ya godewa China, kan kokarin datayi na baiwa Iran rigakafin korona, tare da fatan karfafa alaka lan batun yaki da cutar.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*