?>

Iran: Cikar Shekaru 42 Da Samun Nasarar Juyin Juya Halin Musulunci

An Fara Gudanar Da Jerin Gwanon Babrura Na Tunawa Da Ranar Cin Nasarar Juyin Musulunci A Iran


ABNA24 : Da safiyar yau Laraba ne mahaya babura da motoci su ka yi jerin gwano domin munar zagayowar ranar da juyin musulunci a Iran ya kai ga cin nasara shekaru 42 da su ka wuce.

Ana yin jerin gwanon nan a ciki birane da garuruwa daban-daban na Iran cikin kula da matakan hana yaduwar cutar corona.

A shekarar 1979 ne yunkurin juyin musulunci a karkashin jagorancin marigayi Imam Khumain ya kai ga samun nasarar kifar da gwamnatin tsarin sarauta da shekaru 2500.

A tsawon daron jiya al’ummar Iran din sun rika bayar da kabarbari a saman gidajensu wanda yake tunawa da yadda ta kasance a ranar karshe ta mulkin tsarin sarauta.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni