Ministan kiwon lafiya na kasar Iraki ya bada sanarwan cewa kasarsa ta shiga wata marhala mafi muni na yaduwar cutar korona a kasar. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Abdul-Amir Al-halfi yana fadar haka a jiya jumma’a, ya kuma kara da cewa rashin kula da dokokin hana yaduwar cutar ne yasa mutane suke kara kamuwa da ita.
ABNA24 : Labarin ya kara da cewa a cikin sa’o’i 24 da suka gabata mutane 4,024 suka kamu da cutar wanda ya kai jimillar wadanda suka kamu da cutar a kasar zuwa 661,477.
Sannan a cikin sa’o’i 24 da suka gabata mutane 12 suka rasa rayukansu wanda ya kawo jimillar wadanda suka rasa rayukansu sanadiyyar zuwa 13,232 tun bayan bullarta a shekarar da ta gabata.
A Halin yanzu dai gwamnatin kasar ta kafa dokar hana fita daga karfi 8 na yamma zuwa 5 na safe don rage yaduwar cutar a duk fadin kasar
342/