?>

Hukumar Zaben Kasar Niger Ta Sanar Da Cewa Ta Shirya Tsaf Domin Gudanar Da Zaben Shugaban Kasar Zagaye Na Biyu

Hukumar Zaben Kasar Niger Ta Sanar Da Cewa Ta Shirya Tsaf Domin Gudanar Da Zaben Shugaban Kasar Zagaye Na Biyu

Hukumar zaben ta “ CENI” ta gabatar da wani taron manema labaru da a ciki ta bayyana shirye-shiryenta na gudanar da zaben na shugaban kasa zagaye na biyu wanda za a yi a gobe Lahadi 21 ga watan nan na Febrairu.

ABNA24 : Shugaban hukumar zaben mai zaman kanta Issaka Souna ya bayyana cewa; Za Mu shirya zabe ne domin kasar Niger, ba domin kalubalantar wani dan takara ba.”

Bugu da kari,a yayin taron manema labarun na jiya juma’a, an yi bitar yadda zaben da ya gudan a watan Disamba na shekarar da ta gabata.

Har ila yau Issaka Souna ya ce; Tuni an aike da dukkanin kayan aiki na zaben zuwa dukkanin gundumomi, kuma wakilan ‘ yan takarar biyu suna bin diddigin dukkanin yadda shirye-shiryen suke gudana.

Za a yi gogayya ne a zaben zagaye na biyu a gobe idan Allah ya kai mu a tsakanin Muhammadu Bazum na jam’iyyar PNDS, mai mulki da kuma Muhammadu Usmana na jam’iyyar RDR ta adawa.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni