?>

Hukumar Bada Agaji Ta Red Cross Ta Yabawa Iran Kan Yan Gudun Hijirar Afghanistan

Hukumar Bada Agaji Ta Red Cross Ta Yabawa Iran Kan Yan Gudun Hijirar Afghanistan

Babban darakan hukumar bada Agaji ta kasa da kasa Red cross ya bayyana jin dadinsa game da gudunmawar da iran take bawa yan gudan hijirar kasar Afghanistan sama da miliyan biyar dake kasar, kuma take basu damar shiga kasar

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - mininstan harkokin cikin gida bangaren abin da ya shafi tsaro Majid –Ahamadi a sa’ilin ganawarsa da Robert Mardini babban darakatan kungiyar ta Red Cross ya fadi cewa Akalla iran ta karbi yan gudun hijirar kasar Afghnistan sama da miliyan biyar a kasarta, wadanda suka tsere daga kasar bayan da kungiyar taliban ta karbe iko da mulki a kasar ,

Adaidai lokacin da yakin kasar Ukrain yake barazana game da samar da Abinci a duniya, yada iran take fuskantat kalubale wajen samar da Alkama ga Alummar kasarta, yace Afghanawa dake rayuwar a kasar Iran suna samun Tallafin dala biliyan 5 a duk shekara, kuma an yi musu Allurar rigakafi miliyan 4.5 daga lokacin bullar cutar Annobar Korona Virus zuwa yanzu.

Babban darektan na red Cross yanzu haka yana ziyara ne a kasar Iran a lokacin bukin cika shekaru 100 cur da kafa hukumar Bada Agaji ta kasa da kasa wato Red Cross , yace Iran tana yin abin da ya dace da take barin Afghanawa suna shiga kasarta, kuma ya godewa Iran game da kokarin da take yin a tallafawa yan gudun hijiran kasar Afghnistan.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*